NDLEA ta bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya

Spread the love

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi a jihar Lagos da kuma wasu wurare na daban a cikin jihar.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya ce sun kama ƙwayoyin ne a cikin wasu kayan da ake safara, inda aka kumshe tabar wiwi da hodar iblis da sauyan miyagun ƙwayoyi a ciki.

Sanarwar da Femi Babafemi ya fitar a yau Lahadi ta ce NDLEA ta kama kayan laifin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos.

Kakakin hukumar ta NDLEA ya ce sun kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi da yunƙurin fita da kuma shiga da kayan laifin a ƙasar.

Ya ce jami’an NDLEA sun yi samame a sassa da dama na jihar Lagos inda suka kama mutanen da ake zargin da safarar waɗannan kayan laifi, kuma tuni aka fara bincike.

Hukumar ta sha alwashin ci gaba da zaƙulo masu safarar ƙwayoyi da sauran kayan laifi dangin ƙwayoyi a duk inda suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *