NDLEA Ta Cafke Ma Su Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A London Evening Kano.

Spread the love

Jami’an hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jahar Kano, ta samu nasarar cafke wasu matasa da ake zarginsu da Ta’ammali miyagun kwayoyi, a wajen shakatawa da cin abinci na London evening, dake kan Titin Audu Bako Way Kano.

jaridar idongari. ng, ta game wa idonta yadda jami’an NDLEA , Suka fito da wasu daga cikin Matasan cikin maye , inda aka sanya su a cikin wata farar mota kirar Hillux.

Wajen cin abincin da shakatawar na London evening, gamayyar maza da mata ne ke taruwa, inda ake zargin ana Ta’ammali da miyagun kwayoyi, da kan jefa rayuwar matasan cikin mummunan hali.

Jami’an sunyi wa wajen dirar mikiya da misalin karfe 11:50PM na daren Laraba, inda Suka dinga fito wa daga matasan da ake zargin sun bugu , sakamakon shan miyagun kwayoyin da Suka yi, Ana sanya su a bayan Wata farar mota Hillux.

A kalla dai jami’an sun shafe kusan mimtuna 40, Kafin daga bisani , su tafi a cikin wasu motoci guda hudu da Suka hada da Kananan motoci uku da Hillux guda daya.

Nyesom Wike Ya Zargi Wasu Jamiā€™an Gwamnati Da Yi Wa Tsarin Filayen Abuja Zagon Kasa.

Rahotanni na cewa kan Titin Audu Bako Way da kuma kan Titin asibitin Nasarawa, Ana zargin wasu na amfani da irin guraren cin abincin ko na hutawa , a matsayin makafa wajen aikata laoifuka.

Irin wadancan gurare musamman a yankin Nasararawa, sun yi kaurin akwanakin baya, hukumar Hisbah ta sha yin kama, maza da Mata ake zargin suna yawon banza.

Wasu matan na fitowa daga gidajen iyayensu ba tare da sanin wajen da za suje ba, inda batagarin Mutane ke daukar su , zuwa ire-iren guguraren

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *