NDLEA ta kama kwaya da aka ɓoye cikin injin mota

Spread the love

Jami’an hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Najeriya sun kama wasu tarin ƙwayoyi da aka ɓoye cikin inji wata motar bas a kan babban titin Gbongan zuwa Ibadan.

Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce hukumar ta kuma kama wasu mutum biyu da ta ce sun manyanta bisa zargin safarar ƙwaya a ƙasar.

Babafemi ya kuma ce hukumar ta NDLEA ta kama wata mata mai shekara 26 da ake zargi da safarar abun maye a kwalabe a lokacin samamen da jami’an hukumar suka kai maɓoyarta a jihar Osun.

Sanarwar ta ce ta kama aƙalla lita 16.5 na ruwan kwalaben da kuma tabar wiwi a lokacin samamen.

Ana fargabar gini mai hawa biyar ya ɗanne mutane da dama a Anambra

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *