Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta sanar da kama miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi da kuɗinsu ya haura naira biliyan ɗaya.
Hukumar ta ce ta yi kamen ne a jihohin Legas da Kano da kuma Jigawa, kuma cikin mutanen da aka kama har da wasu mata ‘yan kasar waje uku.
Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya ta zama ruwan dare, inda masharhanta ke cewa iyaye da al’umma baki daya su hada kai wajen yakar matsalar.