Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar kano, ta samu nasarar kama wata mata Mai suna,Harira Idris mai shekaru 50, Aliyu Sale mai shekaru 25, da kuma Abba Sale mai shekaru 33 dukkannin su yan asalin karamar hukumar Kumbotso a jahar kano bisa zargin su da siyar wa da kuma safarar miyagun kwayoyi a birnin jahar.
Mai magana da yawun hukumar Sadiq Muhammad mai gatari ne ya bayyana hakan ga manema labarai , inda ya ce, Harira mahaifiyar Aliyu Sale da Abba Sale ta yi kaurin suna wajen ajiye mu su kayan mayen da suke siyarwa jama’a domin gusar da hankalin su.
Kayan da mayen da aka same su da shi sun hadar da Tabar wiwi, sholisho, madarar sukudayin dadai sauran su.
Yana mai cewar, bayan kayan mayen da aka kama su da shi, an same su da muggan makamai da suke amfani da shi wajen yin rauni ga jami’an tsaro musamman na hukumar NDLEA.
- Yan Sanda Sun Cafke Matashiyar Da Ake Zargi Da Jagorantar Satar Wayoyin Mata A Kano
- Sabuwar 2025: An Tsaurara Matakan Tsaro A Muhimman Wurare A Kano.
Ya kara da cewar, yanzu haka dai suna kan fadada bincike kan lamarin, da zarar sun kammala zasu mika su gaban kotu domin girbar abinda suka shuka
A karshe yayi kira ga hukumar yan sandan kano dasu kawo musu Shamsiyya wadda ta kware wajen yin zamba cikin aminci da satar wayoyin jama’a domin duba kwakwalwar ta.