Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu ya ɗiga alamar tambaya kan yadda ake gaggawa domin amincewa da ƙudurin harajin da shugaban ƙasa Tinubu ya aika majalisa.
Ndume ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da tashar Channels a shirin Politics Today.
Sanatan ya ce a zaɓen 2023, sanatoci 25 ne kawai suka dawo, wanda hakan a cewarsa ke nuna cewa mutane sun fara daina amince da su.
Ya ƙara da cewa yadda ake gaggawar amincewa da ƙudurin na harajin, ya nuna kamar akwai lauje cikin naɗi.
“Ba wai ina da matsala da ƙudurin ba ne, kuma ba wai ina cewa a yi watsi da shi ba ne baki ɗaya, amma tunda gwamnoninmu waɗanda su ne jagororinmu da kuma majalisar tattalin arziki da wasu ɗaiɗaikun mutane sun bayyana cewa akwai buƙatar ƙarin lokaci domin a tattauna, ya kamata a ɗan ƙara lokaci. Me ya sa ake gaggawa?” in ji shi.
Ndume ya ce babbar matsalarsa da ƙudurin ita ce lokacin da aka bijiro da ita, inda a cewarsa bai kamata a ce an kawo maganar ƙudurin ba a daidai wannan lokacin da ƴan Najeriya suke cikin ƙuncin rayuwa.
“Tun kakanninmu uuna biyan haraji a arewa. Don haka ba wai muna tsoron biyan haraji ba ne, duk wani ɗan ƙasa na ƙwarai zai biya haraji, amma gaskiya zuwa da wannan maganar a wannan lokacin bai dace ba,” in ji shi.