Neman belin N10m daga wurin ƙananan yara wauta ce — Kwankwaso

Spread the love

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah wadai da sharuɗan belin da kotu ta sanya wa yaran da ake tuhuma da laifin cin amanar ƙasa a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Kwankwaso, ya ce ƙananan yaran da alamu suka nuna suna fama da matsananciyar yunwa da rashin isasshiyar lafiya, amma gwamnati ta tsare su tsawon lokaci, tare da azabtar da su, madadin magance matsalolin da ke addabar ƙasar.

Kwankwaso, ya kaɗu kan sharuɗan da kotun ta gindaya wa yara , inda ya ce hukuncin cin zarafin ɗan Adam ne.

Ya ce, “Na yi mamakin jin cewa an gurfanar da ƙananan yara 67 a gaban kotu a Abuja da zargin shiga zanga-zangar #EndBadGovernance.

“Waɗannan yara da suke shan wahala da rashin lafiya, suna fuskantar halin ƙaƙa-na-ka-yi wanda kamata ya yi a ce suna makaranta.

“Gurfanar da yara masu yawa haka abun mamaki ne, wanda ya saɓa wa ƙa’idodin kare haƙƙin ɗan Adam.

“A matsayinmu na shugabanni, wajibi ne mu kare marasa galihu, musamman yara, mata, tsofaffi, da kuma mabuƙata. Bai kamata gwamnati ta ke take haƙƙin ɗan Adam ba.

“Na yi takaicin sharuɗa tsaurara da aka gindaya wajen bayar da belinsu. Abun mamaki ne a ce an buƙaci matashi ya kawo Naira miliyan 10 da kuma ma’aikacin gwamnati mai matsayi na 15 don ba da belinsa.

“Dokar kare haƙƙin yara ta shekarar 2003, sashe na 11, ta tabbatar da cewa a kare mutuncin kowane yaro daga duk wani nau’in cutarwa, zalunci, ko rashin kulawa,” a cewar Kwankwaso.

Kwankwaso ya yi kira ga hukumomi da su duba wannan lamari tare da sakin yaran su koma wajen iyayensu.

“Ina kira ga hukumomi su duba lamarin tare da barin yaran su koma wajen  iyayensu domin su zama ’yan ƙasa nagari.

“Sannan, ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mayar da hankali wajen magance matsalolin ’yan bindiga, sace-sace, Boko Haram, matsalar wutar lantarki, da kuma tsauraran manufofin tattalin arziƙi, maimakon tsare ƙananan yara.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *