Kwamitin bincike na Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya, NHRC ya kafa ya wanke sojojin Najeriya bisa zarginsu da tilasta zubar da cikin mata aƙalla 10,000 a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Shugaban kwamitin binciken, Abdul Aboki – wanda tsohon alƙalin kotun ƙolin ƙasar ne, tare da sauran mambobin bakwai, sun bayyana zargin da cewa ”ƙarya ce maras tushe” da ke cikin wani rahoto na musamman da wata kafar yaɗa labaran ƙasar waje ta wallafa.
A zaman ƙarshe da kwamitin ya yi ranar Juma’a a Abuja, ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da wannan zargi da ke ƙunshe cikin rahoton.
“Dangane da batun tilasta zubar da ciki, kwamitin bai samu wata hujja da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun aikata abin da ake zargnsu da shi na tilasta zubar da ciki a asirce na kusan mata 10,000 a yankin arewa maso gabas, babu wata hujja da ta nuna hakan a iya binciken da muka yi,” kamar yadda babban sakataren hukumar NHRC, Tony Ojukwu ya bayyana.
A watan Disamban 2022 ne kamfanin dillancin labarai na Reuters cikin wani rahotonsa ya zargi sojojin Najeriya da aikata laifukan keta haƙƙin bil-adama – ciki har da zargin tilasta wa mata da ‘yan mata aƙalla 10,000 zubar da ciki – a lokacin da suke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas tun 2013.
Rahoton ya ce an zubar da cikin ne ba tare da so ko izinin matan ba.
BBCH