Ni ma na sha yin zanga-zanga amma ta lumana – Bola Tinubu

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce shi ma ya sha shiga zanga-zanga a lokacin mulkin soja “amma ba tare da tashin hankali ba”.

Shugaban na magana ne yayin da gwamnatinsa ke ta roƙon masu shirya zanga-zanga game da tsadar rayuwa da su ƙara mata lokaci don maganace matsalolinsu cikin ruwan sanyi.

“A lokacin mulkin soja, mun yi adawa da ‘yan kama-karya, kuma ina cikin mutanen da suka dinga zanga-zangar lumana ba tare da ƙone-ƙone ba,” a cewar shugaban lokacin da yake karɓar baƙuncin Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills Jr. a yammacin yau.

Ya ci gaba da cewa “mun yi bakin ƙoƙarinmu wajen tabbatuwar shekara 25 ta mulkin dimokuraɗiyya a jere kuma zan yi cigaba da rainon wannan dimokuraɗiyyar”, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *