Nigeria: Tsofaffin Yansanda Na Zanga-zanga A Abuja

Spread the love
Abuja

Jami’an ƴansandan Najeriya da suka yi ritaya, waɗanda ke karkashin tsarin fansho na karo-karo (contributory pension scheme), suna zanga-zanga a harabar majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja.

Tsofaffin jami’an da suka tattaru a harabar majalisar suna korafi ne a kan rashin biyansu kuɗinsu na fansho na wata da watanni.

Tsofaffin ƴansandan da ke wakiltar rassansu na jihohi daban-daban suna kokawa da irin wahalar da suke ciki a kan ƙin biyansu haƙƙin nasu da hukumar fansho ta ƙasar ta yi.

Haka kuma suna kira ga gwamnatin tarayya da ta fitar da su daga cikin wannan tsari na fanshon na karo-karo.

Ko a watan Satumba na 2021, ƴansanda da suka yi ritaya daga jihohi 27 a Najeriyar sun hallara a majalisar dokokin da ke Abuja, inda suke neman a biya su kuɗin fanshonsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *