NJC Ta Aikawa Alkalai 3 Da Takardar Gargadi Tare Da Hana Ciyar Dasu Gaba

Spread the love
NJC
NJC

A yayin zamanta na 105 daya gudana tsakanin ranaikun 15 da 16 ga watan Mayun da muke ciki, Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Najeriya (NJC) karkashin jagorancin alkalin alkalan kasar, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ta yanke shawarar aikewa da takardun gargadi ga Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da takwaransa na babbar kotun jihar Delta, Mai Shari’a Gb Brikins Okolosi.

Sanarwar da Daraktan Yada Labaran njc, Soji Oye, ya fitar tace an gargadi Mai Shari’a Ekwo akan yin amfani da alfarmarsa ta zama alkali wajen bada wani umarnin dakatar da daukar mataki a bisa kuskure a shari’ar dake tsakanin Juliet Ebere Nwadi Gbaka da wasu mutun 2 da kamfanin makamashi na Seplat Energy PLC da wasu mutum 12.

Haka kuma an haramta daga likkafar Mai Shari’a Ekwo zuwa mataki na gaba tsawon shekaru 2.

Shi kuwa Mai Shari’a Gb Brikins-Okolosi na babbar kotun jihar Delta, an mika masa takardar gargadin ne akan gazawarsa wajen yanke hukunci cikin lokacin da doka ta amince a shari’ar Joseph Anene Okafor da bankin Skye bayan da lauyoyin bangarorin 2 sun gama amincewa da rubutattun bayanan shari’ar.

Shima Mai Shari’a Brikins-Okolosi an haramta daga likkafarsa zuwa mataki na gaba tsawon shekaru 3.

Haka kuma NJC ta gargadi Mai Shari’a Amina Shehu ta babbar kotun jihar Yobe domin ta bada izinin mallaka daya baiwa bangaren wanda ake kara damar mallakar kadara a wata shari’a bayan babu hukuncin wata kotu daya bata damar bada iznin.

A yayin zaman nata majalisar ta nazarci rahotannin guda 2 na kwamitocin fara nazarin rubutattaun korafe-korafen da aka shigar akan alkalan manyan kotunan tarayya dana jihohii tare da tace 35 daga cikinsu tare kafa kwamitoci 8 da zasu zurfafa bincike akan korafe-korafen da kwamitocin suka gano suna da mahimmanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *