NLC Ta Rufe Ofishin NERC

Spread the love

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe ofishin Hukumar Wutar Lantarki (NERC) domin nuna adawa da karin kuɗin wuta da aka yi wa ’yan Najeriya.

A yau Litinin ne ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC da takwararta ta TUC ke dafifi a harabar ofishin hukumar kula da lantarki ta ƙasar NERC da na kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki a faɗin Najeriya domin nuna adawa da ƙarin kuɗin wuta a ƙasar.

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin kuɗin wuta ga ƴan rukunin A masu samun wuta tsawon sa’a ashirin a rana.

Lamarin ya fusata al’umma ganin irin halin matsi da ƴan Najeriya ke ciki.

Duk da cewa NERC ta yi nazari kan ƙarin kuɗin amma gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce za su mamaye harabar ofishin hukumar da kuma kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki bayan da wa’adin da suka bayar na ranar Lahadi don hukumar ta soke ƙarin kuɗin ya cika.

Ƙarin kuɗin wutar na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya sakamakon hauhawar farashi da kuma ƙalubalen da ƴan Najeriya suke fuskanta sanadin janye tallafin man fetur.

Sai dai a lokacin da yake kare matakin, ministan lantarki, Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya za ta biya kimanin naira miliyan 1.8 a matsayin kuɗin tallafi na lantarki a kasafin kuɗin 2024.

Ya bayyana cewa dokar lantarki ta 2023 ta ba da izinin a yi nazarin kuɗin wuta sau biyu a shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *