NNPCL bai ba mu izinin bai wa dillalai mai ba – Ɗangote

Spread the love

Matatar Ɗangote ta ce har yanzu ba ta karɓi kuɗi daga ƙungiyar dillalan mai ta Najeriya Ipman ba domin sayen tataccen mai.

Wata sanarwa da matatar ta fitar a shafin X, ta ce ana tattaunawa da Ipman sai dai ta ce bai dace mambobin Ipman su nuna cewa suna fuskantar matsala ba wajen sayen tataccen mai daga matatarmu kasancewar “babu wata alaƙar kasuwanci ta kai tsaye da Ipman.

A cewar matatar ta Ɗangote, cikin sanarwar da jami’inta na hulɗa da jama’a, Anthony Chiejina ya sanyawa hannu, “an biya kuɗin da ake magana a kai ta hannun kamfanin mai na NNPCL, ba wurinmu ba.”

NNPCL ba ta amince da kuɗin ba, kuma ba ta ba mu izinin sayar da man fetur ga Ipman.”

Matatar ta ce “muna son mu jaddada cewa za mu iya wadatar da Najeriya da duk albarkatun mai har da man jirgi.”

“A yanzu, muna iya fitar da tirela 2,900 na mai duk rana kuma muna fitar da albarkatun mai ta hanyar ruwa.” in ji matatar Ɗangote.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *