NNPCL ya fara jigilar iskar gas zuwa China da Japan

Spread the love

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya fara jigilar iskar Gas zuwa Japan da China ta jirgin ruwa.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa, an cimma wannan buri ne ta hanyar haɗin gwiwar wasu rassan kamfanin wato NNPC LNG Ltd da NNPC Shipping Ltd.

Kamfanin NNPCL ya fara isar da iskar gas a ranar 27 ga Yuni, 2024 daga jirgin ruwa mai tsawon mita 174,000 Grazyna Gesicka a Futtsu, wani birni da ke Japan.

Bayan haka, kamfanin ya faɗada ayyukansa zuwa ƙasar China, inda ya kai wani kaya na iskar gas ta jirgin ruwa.

Soneye ya bayyana cewa tsarin jigilar iskar gas ta jirgin ruwa na buƙatar babban matakin ƙwarewa da inganci.

NNPCL yana kasuwancin iskar gas tun daga 2021, lokacin da ya fara sayar da iskar gas ɗin a karon farko a watan Nuwamba na shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *