Kano:NNPP Ta Canja Dan Takarar Shugabancin Karamar Hukumar Kumbotso.

Spread the love

Jam’iyyar NNPP a Kano ta canja dan takarar shugaban karamar hukumar Kumbotso Ali Hard Worker Dan Maliki.

Jam’iyyar NNPP ta sauya wanda zai yi mata takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Kumbotso a zaɓen Ƙananan Hukumomin mai zuwa.

Wata majiya mai tushe a jam’iyyar NNPP ta tabbatar wa Freedom Radio cewa an sauya Ali Musa Hard Worker da Ghali Abdullahi Basaf saboda wasu dalilai.

Ghali Basaf tsohon Shugaban Ƙungiyar Kwankwasiyya Reporters ne na ƙasa kafin daga bisani Gwamnan Kano ya naɗa shi a maitaimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai.

Har zuwa loacin hada wannan rahoton babu wata sanarwa daga jam’iyar kan dalilin ta na canja dan takarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *