Jama’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta sanar da dakatar da Sanata Kawu Sama’ila da wasu ƴan majalisar tarayya uku daga jihar ta Kano.
Ƴan Majalisar da jam’iyyar ta kora su ne:
- Suleiman Kawu Sumaila – Sanata mai wakiltar Kano ta kudu
- Aliyu Sani Madakin Gini – Ɗan Majalisa wakilai daga mazaɓar Dala
- Sani Abdullahi Rogo – Ɗan majalisa mai wakiltar Karaye da Rogo
- Kabiru Alhassan Rurum – Ɗan majalisar wakilai daga mazaɓar Rano, Kibiya da Bunkure
A bayanin da ya yi wa manema labaru a ranar Litinin a Kano, shugaban jam’iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin ne bayan samun ƴan majalisar da laifin ayyukan zagon ƙasa ga jam’iyyar.
- Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji
- Shugaban APC A Kano Abdullahi Abbas Da Fa’izu Alfindiki Sun Bayyana A Gaban Kotu Kan Zargin Batanci Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
A cikin bayaninsa, Dungurawa ya ce ƴan majalisar waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP suna gudanar da ayyuka da suka ci karo da manufofi da ƙudurorin jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne yayin da har yanzu jam’iyyar ke ci gaba da fama da rikicin shugabanci.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban NNPP na jihar Kano ya ce yanzu jam’iyyar ta kafa kwamiti wanda zai duba batun dakatarwar wanda zai gayyaci sanatan da sauran ƴan majlisar wakilai uku domin yin bayani kan zargin da ake yi musu.
Wane laifi ƴan majalisar suka aikata?
An fara ɗora ayar tambaya kan biyayyan ƴan majalisar ga jam’iyyar ne bayan bikin da aka gudanar na auren ƴan Sanata Kawu Sumaila.
Dungurawa ya ce Sanata Kawu Sumaila ya gayyaci manyan ƴan jam’iyyar APC mai mulkin ƙaar, kuma mai hamayya a jihar Kano zuwa wajen bikin, ba tare da ya gayyaci shugabannin jam’iyyar NNPP ba.
“Abdullahi Ganduje na wajen, Ibrahim Shekarau na cikin wurin, saboda haka irin wannan akwai takaici”
“Wane irin saƙo ko darasi suke koya wa ƴan baya ke nan?
“A matsayina na shugaban jam’iyyar NNPP bai gayyace ni ba, shi ne muka ga hakan bai dace,” kamar yadda Dungurawa ya shaida wa BBC.
Dungurawa ya kuma yi zargin cewa sanatan da ƴan majalisar tarayyar ba su halarci taron da jam’iyyar ta NNPP ta gudanar a Abuja ba.
“Mun yi taro kwanan nan a Abuja ba su je ba kuma ba su turo wakilci ba.”