Jam’iyar NNPP ta Dakatar da sakataren Gwamnatin jahar, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, da kuma kwamishinan sufuri Muhammed Diggol.
Wannan na Zuwa ne Yan mintuna kadan da Gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf , ya jagoranci zaman sulhunta sabanin da aka samu Tsakanin sakataren Gwamnatin jahar Dr Abdullahi Baffa Bichi da kuma Dan takarar shugaban karamar hukumar Bichi Hamza Maifata.
Shugaban jam’iyar NNPP na jahar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ne ya sanar da Dakatar su , a ranar Litinin.
A cewar sanarwar dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafen da dama Wanda yayan jam’iyar a mazaba da kuma karamar hukumar suka shigar.
Dungurawa ya kara da cewa , sun Yi hakan ne sakamakon rashin mutunta jam’iyar da shugabannin ta da suke Yi.
Kwanaki kadan ya rage a gudanar da Zaben Kananan hukumomin jahar Kano, a ranar 26 ga watan Oktoba 2024.
Sai dai wasu masu sharshi kan al’amuran yau da kullum na cewar hakan ba zai rasa nasaba da yadda aka fitar da Yan takaran shugabancin kananan hukumomi ba.