Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Kano KANSIEC ayyana ƴan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomi 44 da na kansiloli 484 da aka gudanar a jihar yau Asabar.
Shugaban hukumar zaɓe a jihar, Farfesa Sani Lawan Malunfashine ya bayyana haka bayan kammala tattara sakamakon zaɓen.
Jam’iyyu shida ne dai suka shiga zaɓen da aka yi ta kai ruwa rana saboda umarnin kotuna daban-daban da ke cewa kada a yi zaɓen da kuma wadda ta ce a yi.