NSCDC Ta Kama Matasan Da Ake Zargi Da Yunkurin Halaka Jami’in Bijilanti A Kano.

Spread the love

Hukumar tsaron civil defence reshen jahar Kano, ta samu nasarar kama wasu matasa 2, bisa Zargin su da tayar da fitina, kwace da satar kayan al’umma dake unguwar Danbare , a karamar hukumar Kumbotso.

Kakakin hukumar tsaron civil defence na jahar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labari.

Wadanda ake Zargin sun hada da, Mustapha Jibrin da kuma Yusuf Sanusi , dukkansu mazauna unguwar Danbare.

An kama su ne bayan Samun sabani da Wani jami’in bijilanti, Inda matasan suka Yi dauki makamai da suka hada da wukake kirar Faranka da Danbida, har suka biyo jami’in bijilanti don su halaka shi kamar yadda rahotanni suka nuna.

Yanzu haka dai hukumar ta ce bincike ya kusa kammaluwa kuma da zarar an kammala za a Gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Haka zalika ana zargin matasan da addabar mutanen Danbare da yawan sata harma da kwace, Inda hukumar ta ce za ta ci gaba da tabbatar da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *