NSCDC Ta Kama Mutane 2 Da Zargin Fashi Da Makami A Kano

Spread the love

Hukumar tsaron civil Defence ta kasa reshen jahar Kano, ta kama wasu matasa biyu dauke da bindiga kirar gida da harsashin ta da kuma Wukake guda 2, inda ake zargin suna aikata laifin fashi da makami, sace-sace da kwacen wayoyin jama’a, da sauran laifuka a sassan jahar.

Kakakin hukumar tsaron civil defence reshen jahar Kano, SC Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce wadanda ake zargin sun hada da , Abdullahi Ibrahim da Faisal Iliyasu dukkansu mazauna jahar.

Yanzu haka dai hukumar tsaron civil defence din ta ce matasan suna tsare a hannun su kuma da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

A karshe hukumar ta ce ta ba za komar neman sauran mutane biyun da suka gudu a lokacin da suka ga jami’an tsaron civil defense na gudanar da aikin sintiri kamar yadda idongari.ng, ta ruwaito.

Saurari muryar wadanda ake zargin da kuma ta Kakakin hukumar tsaron civil defence reshen jahar Kano, SC Ibrahim Abdullahi..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *