NSCDC Ta Kama Mutane 2 Da Zargin Sojan Gona Da Sunan Hukumar A Kano

Spread the love

Hukumar tsaron civil defence ( NSCDC) reshen jihar Kano ta samu nasarar kama wasu mutane biyu, bisa zarginsu da bayyana kansu a matsayin jami’an hukumar inda suke yin sojan gona tare da karbar kudade a hannun al’umma ta hanyar yi mu su barazana.

Wadanda ake zargin sun hada da Muhammad Sarari dan shekaru 43 mazaunin Goron Dutse da kuma Madaki Zaharaddin mai shekaru 32 mazaunin Hotoro dukaa jihar Kano.

Kakakin hukumar tsaron civil defence na jihar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a ranar Litinin

Jami’an Civil Defence na karamar hukumar Taruni suka samu nasarar kama su, da zargin bin manayn ma’aikatun gwamnati a Kano,inda suke karbar kudade tare da zuwa wata kafar Telebijin suka nemi a basu kudi.

Hukumar ta ce da Zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *