NSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Damfarar Mata Da Zummar Samar Mu su Da Aiki A Kano

Spread the love

Hukumar tsaron Civil Defence reshen jahar Kano, ta samu nasarar kama wani mutum mai suna Mu’azu Mohammed Ibrahim, da ake Zargin ya kware wajen damfarar jama’a ta hanyar karbar kudadensu domin samar mu su aiyukan Yi a hukumomin jihar Kano.

Kakakin hukumar tsaron Civil Defence reshen jahar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labari.

Ibrahim Idris ya ce Wanda Ake Zargin ya bayyana kansa a matsayin mai fada aji ne a jahar tare da nuna cewa Yana da alaka da wasu hukumomin tsaro, Amma sojan gona yake Yi.

A kalla dai mata 10 ne suka Yi korafi akan sa bayan ya karbe mu su kudade da zummar zai samar mu su da aikin Yi.

Wanda Ake Zargin ya amsa cewar hakika ya karbi kudi sama da naira Miliyan daya da Dubu dari biyu (1.2m).

Ya kara da cewa, ya karbi kudin hannu da hannu Amma akwai wadanda wata Mai suna Ummi ta karba ta bashi.

Hukumar ta kara da cewa tuni jami’an su da suke kula da binciken laifuka sun kammala bincike , kuma ya tabbatar da cewar da ya karbi kudin , Amma karya yake Yi, Sannan za a Gurfanar da shi a gaban Kotu don ya fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *