Ƙungiyar Organization for Development and Political Matrix Nigeria (ODPM Nigeria) ta gabatar da taron tattaunawa na musamman da matasa a ƙaramar hukumar Bichi.
Ƙungiyar ta samu haɗin gwiwar kungiyar majalisar matasa ta kasa reshen ƙaramar hukumar Bichi (NYCN) domin gabatar da muhimmin taron.
A yayin taron, an tattauna batun matsalar da tafi damun Jihar Kano kan tsaro da ma ƙasa baki ɗaya tare da zaƙulo hanyoyin da ƙungiyoyi irin ODPM Nigeria na matasa za su bada gudunmawa wajen kawo ƙarshen matsalar a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
ODPMNigeria ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin matasa da hukumomin tsaro, tare da kira ga matasa su kasance masu bayar da shawara da kuma taka rawar gani wajen samar da mafita maimakon su zama cikin masu haifar da matsalar.
An kuma yaba da irin goyon bayan da Ƙungiyar Majalisar Matasa ta Ƙasa (NYCN) reshen Bichi ta bayar, wanda ya tabbatar da nasarar taron.
Masu halarta sun bayyana gamsuwarsu tare da sha’awar ganin irin waɗannan tarurruka suna ci gaba da gudana a sauran yankunan jihar Kano.
Taron ya ƙare da kira ga kowanne matashi da ya kasance jakadan zaman lafiya, tare da yin aiki kafada da kafada domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Kano da Nijeriya gaba ɗaya.