Okpebholo Na APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jahar Edo.

Spread the love

Hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamman jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar 21 ga watan Satumba.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar – wanda kuma shi ne shugaban jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Minna – Farfesa Farouk Adamu Kuta ne ya bayyana sakamakon a zauren tattara sakamakon da ke shalkwatar hukumar zaɓen jihar.

 

Farfesa Kuta ya ce Monday Okpebholo ya yi nasarar lashe zaɓen bayan samun ƙuri’a 291,667, inda ya doke babban abokin karawarsa, Asuerinme Ighodalo na jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, wanda ya samu ƙuri’a 247, 274 a zaɓen.

‘’Bayan samun ƙuri’u mafi rinjaye tare da cika duka sharuɗan da hukumar zaɓe ta gindaya, Monday Okpebholo na APC ya lashe zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar ranar 21 ga watan Satumban 2024’’, in ji Farfesa Kuta.

Sakamakon zaɓen ya nuna Sanata Okpebholo ya lashe ƙananan hukumomin jihar 11 daga cikin 18, yayin da mista Ighodalo ya samu ƙananan hukumomi bakwai.

Zaɓen ya kasance wani fage na nuna ƙarfin siyasa tsakanin manyan jagororin siyasar jihar biyu, tsohon gwamna, kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Adams Oshimole da ke goyon bayan Monday Okpebholo, da kuma gwamnan jihar Godwin Obaseki da ke goyon bayan mista Ighodalo na PDP.

Tun da farko dai jam’iyyar PDP ta bayyana zargin sauya sakamakon zaɓen wasu rumfuna, zargin da hukumar zaɓen ƙasar ta ce za ta yi bincike a kai.

Wane ne Monday Okpebholo?

An haifi Monday Okpebholo a ƙauyen Udomi na ƙaramar hukumar Esan da ke tsakiyar jihar a shekarar 1970.

Ya fara harkokin kasuwanci kafin daga baya ya koma siyasa.

Sabon gwamnan mai shekara 53, kafin yanzu shi ne ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Edo ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan ƙasar ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Okpebolo ya samu goyon bayan tsohon gwamnan jihar, kuma jagoran APC a jihar Adams Oshiomhole, lamarin da ya sa masu sharhi ke ganin ya taimaka masa wajen zama gwamnan jihar.

Mista Monday ya alƙawarta kyautata kiwon lafiyar mata da ƙananan yara da tsofaffi da ‘yan ritaya ta hanyar inshorar lafiya.

Haka kuma ya alƙawarta inganta harkokin ilimi da haɓaka tattalin arziki da tsaro a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *