Osimhen zai buga wasan Najeriya da Afrika ta Kudu

Spread the love

Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta ce an tabbatar da cewa ɗan wasanta na gaba Victor Osimhen na da lafiyar da zai iya buga wasan da kasar za ta yi na kusa da na karshe da Afrika ta Kudu.

An dai fitar da hotunan atisayen ƙungiyar ta Super Eagle a ƙasar Cote d’Ivore, inda aka nuno ɗan wasan na atisayen tare da sauran takwarorinsa.

Rundunar yan sandan Kano ta kaddamar da kwamitin mutane 11 na dokokin aikin yan sanda (Force Order 20).

Babu gaskiya kan cewa ƴan Najeriya na fuskantar barazana a Afirka ta Kudu

An dai shiga fargaba bayan da aka yi tunanin cewa ɗan wasan zai iya gaza buga wasan na gobe Laraba bayan da a jiya Litinin ya gaza bin sauran ƴan ‘uwansa ƴan wasan Najeriya zuwa birnin Bouake inda za su buga wasan.

Najeriya dai ta buga dukkanin wasanninta na rukuni da matakin ƴan 16 da na kwata-fainal ne a filin wasanni da ke Abidjan, babban birnin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *