Ramadan: Mun kaddamar da jami’an bijilanti na musamman don dakile aiyukan batagari a Kano.

Spread the love

Rundunar bijilanti ta jahar Kano, ta ba da tabbacin taimaka wa hukumomin tsaron jahar wajen dakile aiyukan batagari, musamman a wannan lokaci na watan Azumin Ramadana.

Kakakin rundunar bijilantin ta jahar Kano, Kamalu Jibrin Sudawa, ne ya bayyana hakan ta cikin sakon faifen muryar da ya aike wa da Jaridar Idongari. ng, a birnin Kano.

Kamalu Sudawa, ya ce za su ci gaba fadada sintiri a lungu da sako na fadin jahar Kano, kamar yadda kwamandan bijilanti na jahar Kano, Alhaji Muhammed Shehu Rabi’u, ya tashi hakan wajen sanya ido a ko Ina.

Gobara Ta Tashi A Tashar Lantarki Ta Ɗan Agundi A Kano.

Watan Ramadan: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bada Umarnin Garkame Gidajen Gala A Jahar Kano

Ya Kara da cewa, za su bude wani sabon ofishi domin dakile duk wani yunkuri da zai ba wa Musulmi cikas wajen gudanar da ibadarsu.

Ofishin an Samar da shi a yankin Tudun Bojuwa Rejiyar Lemo, domin Fara aikin jami’ai na musamman, na rundunar bijilanti ta jahar Kano, karkashin Kwamandan sintiri OC Mansur Abdullahi Fagge.

Jami’an za su taimaka wa hukumomin tsaro musamman jami’an yan sanda wurin sanya ido don gano inda batagari suke , da kuma dakile duk wani yunkuri da zai ba wa al’ummar musulmi cikas wajen gudanar da ibadarsu.

A karshe ya yi kira ga al’ummar jahar Kano, su Ci gaba da ba wa rundunar bijilanti hadin Kai domin kara inganta tsaro a fadin jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *