Mataimakiyar babban sakataren jam’iyyar ANC Nomvula Mokonyane ta sanar wa manema labarai a cibiyar kirga kuri’un zaɓen da aka gudanar a Afrika ta kudu cewa shugaba Cyril Ramaphosa ba zai sauka daga mukaminsa a matsayin shugaban jam’iyyar ba duk da rashin kyakkyawan sakamakon zaɓen da jam’iyyar ta samu.
Da aka tambaye ta game da yuwuwar tattaunawar hadin gwiwa, Mokonyane ta bayyana cewa, a halin yanzu, jam’iyyar ba ta shiga tattaunawa da wasu jam’iyyu ko ƙungiyoyi ba.
Ta kuma bayyana cewa a yau ne shugabannin jam’iyyar ANC za su yi taro domin tattauna sakamakon zaben da ake yi a yanzu.
An shirya gudanar da taron manema labarai da yammacin ranar Asabar.
- EFCC ta kama wasu mutum 40 da zargin damfara ta Intanet a Akwa Ibom
- Yan Sanda Sun Gargadi Jama’a Su Guji Yada Labaran Karya Cewar Sarkin Kano Na 15 Zai Yi Sallah A Kofar Kudu