Ranar 8 ga Nuwamban 2025 za a yi zaɓen gwamnan Anambra – INEC

Spread the love

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta sanya ranar 8 ga Nuwamban 2025 domin gudanar da zaɓen jihar Anambra.

Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a yau Alhamis a shafukanta na sada zumunta.

“Hukumar ta amince da ranar Asabar, 8 ga Nuwamban 2025 domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra na 2025.

“Domin cika ƙa’idar fitar da sanarwar da zaɓen na kwana 260 kafin zaɓe, za a wallafa sanarwar zaɓen a ranar 13 ga Nuwamban 2024. Jam’iyyu za su gudanar da zaɓukan fid-da-gwani ne tsakanin 20 ga Maris zuwa 10 ga Afrilun 2025, sannan za a buɗe shafin sanya sunayen ƴantakara a ranar 18 ga Afrilu zuwa 12 ga Mayun 2025, sannan a fitar da sunayen ƴantakara na ƙarshe a ranar 9 ga Yunin 2025.

“Za a fara yaƙin neman zaɓe a ranar 11 ga Yunin, sannan a gama a ranar 6 ga Nuwamba, sannan a gudanar da zaɓe a ranar 8 ga Nuwamban 2025,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *