Ranar Yara Ta Duniya: Gidauniyar Tallafa Wa Mabukata Ta Bukaci Al’umma Su Kula Da Tarbiyar Yara.

Spread the love

Ranar Yara ta Duniya 27/May/2024.

Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation na Kira ga al’umma da su kula da tarbiyyar Yara masu tasowa da Kuma Samar musu da ilmi da madogara Mai kyau da zata samar da manyan gobe.

Gidauniyar tana da dalibai na musanman Yara kanana Marayu tare da iyayen Marayu Wanda suke karkashinta, Akan zaburar dasu Kan jajircewa Dan zama Yara manyan gobe masu tarbiyya da cimma burin da suke son kasancewa anan gaba.

Sannan shugaban gidauniyar Amb Auwalu Muhd Danlarabawa ya Kara yin Kira ga iyaye da suka barin Yaransu a titi ba kulawa sannan basa iya daukar nauyin su dan su samu ilmi, da masu tura Yaransu Barace Barace suna kwana akan titi, Wanda Daga bisani suke fadawa harkoki na Shaye Shaye da saca-sace a cikin al’umma.

Haka Kuma Muna Kara Kira ga Gwamnati data mayar da hankali wajen inganta rayuwar kananan Yara Wanda basa zuwa makaranta da Kuma Magance yawaitar Yara a titi masu Barace Barace da yawon bola.

Sannan shugaban gidauniyar Amb Auwalu Muhd Danlarabawa ya Kara yin Kira ga al’umma suyi kokari Suma a unguwannin su wajen Sanya idanu akan tarbiyyar Yara da Basu tarbiyya da dakile dukkan wasu harkoki da Kan iya gurbata rayuwar Yara a unguwanni

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *