Kwanan baya ne kadan tsohon dan Majalisar Wakilai Ta Kasa, daga Karamar Hukumar Tarauni, a Kano, Hafizu Kawu ya shirya wata bitar karawa juna ilimi kan hanyoyin da ya kamata a bi dan tsaftace harkokin soshiyal midiya (Social Media), musamman ga ‘yan siyasa da magoya bayansu. An shirya bitar ne ta karkashin Hafizu Kawu Media Team tare da hadin gwuiwar Majalisar Malamai Ta Kasa, Reshen Jihar Kano. Ga kadan daga cikin tattaunawar da wannan kafa ta yada labarai ta yi da shi kan taron :
1. Tambaya : Da farko Alhaji Hafizu Kawu, tsohon dan Majalisar Wakilai Ta Kasa daga Karamar Hukumar Tarauni, mun ga ka shirya wata bita ta musamman karkashin Hafizu Kawu Media Team, tare da hadin gwuiwar Majalisar Malamai Ta Kasa, Reshen Jihar Kano, kan abinda ya shafi tsaftace amfani da soshiyal midiya tsakankanin al’umma musamman yan siyasa. Wane abu ne ya sa ka wannan tunanin mai muhimmancin gaske kuwa?
Alhamdulillahi Rabbil Aalamin.
Dukkan godiya da yabo ya tabbata ga Allah Mai Kowa Mai Komai.
Wannan program da ‘yan media dina muka zauna tare da su mu ka yi tunani mun yi duba da yanayin da social media ta tsinci kanta a wannan tsari ko sabga ta siyasa. Shi ya sa mu ka ce ya kamata mu yi taro na bita domin wayar da kai domin a samu fahimta a samu hadin kai kuma a tsabtace wannan tsari na social media. Saboda in ka kalla shi kansa bature ya kirkiri wannan social media ne domin sada zumunta da kuma isar da sako cikin sauki.
Amma mu ‘yan siyasa se muke amfani da ita wurin yada fitina ko kuma haddasa husuma. Wadansu ma har take kaiwa a na cin zarafi, a na cin mutunci a na sa-in-sa wanda Addinin Musulunci ya hana. Shi ya sa mu ka yi tunani muka ce bari mu kira malamai saboda sune magada Annabawa kuma sune wadanda in su ka fada a ke ji domin mu hadu gaba daya, da ‘yan jam’iyyar adawa da ‘yan jam’iyyar hamayya mu fahimtar da juna. Mu karawa juna sani sannan malamai su gaya mana. Kamar shi Farfesa tun da fanninsa ne kuma ya san wannan kuma shi ba ma dan siyasa ba ne, amma mu ka kira shi domin ya gaya mana amfanin ita wannan social media da kuma yadda ya kamata ta kara kawo mana hadin kai.
A matsayinmu na musulmai kamata ya yi mu dinga yada ilimi mu na yada fahimta. Siyasa a gefe take amma zumunci da mutuntawa yafi harkar siyasa.
Yau zamantakewar tare ta fi a zo a ce a na rigingimu tun da yau in mutum ya ce ya daina siyasa ai za a ci gaba da zumunci. Amma wadansu kan dauki siyasar ma ta fi zumuncin. A zo a ci mutuncin juna a baci juna. Shi ya sa mu ka yi nazari mu ka yi tunani mu ka hada taro kuma mu ka gayyaci duk ‘yan jam’iyyar hamayya a wannan jiha ta mu mai albarka domin mu karawa juna sani sannan mu tsaftace wannan tsari. Kuma mu gina sabuwar alaka, kuma mu gina sabuwar fahimta kuma kowa ya tallata nasa gwanin ko kuma ya tallata ta sa jam’iyyar ko kuma a tallata gwamnati ba tare da cin mutuncin juna ko an sami wata kokawa ko wani kokwanto ko an kawo matsaloli wandanda za su shafi harkar addini ita da kanta.
2. Tambaya : Yaya ka ga ra’ayin jama’a kan shi wannan gagarumin taro da ku ka shirya?
To wannan amfaninsa shi ne kara tsaftace ita harkar social media da karawa juna sani, sannan kuma da shi kansa kara sani da kara hada zumunci tsakanin jam’iyyu da kuma kara fahimtar da juna da kuma sanin ma me Allah Subhanahu Wata’Ala Ya ce, me Addininmu ya ce kan zamantakewa musamman akan abun da ya shafi harkar adawa ta wannan kafafen sada zumunta da ake dashi. Shi ya sa a ka yi wannan bita kuma ta yi matukar ba da ma’ana. Kuma mutane sun yi farin ciki kuma irin wadanda su ka dinga kira sun nuna mana cewa ya kamata sun zo an yi da su. Wadansu ma su na ta cewa da sun sani da sun zo tunda abun ya burge su. Su ka ce saboda ba a taba samun irin wannan ba, wannan shi ne na farko da a ka yi irin sa a ka kawo kowa da kowa da yake da ruwa da tsaki a harkar social media da harkar siyasa. Kuma ko ba komai an sada zumunci tunda ba a ko ina ne za ka ga an samu irin wannan haduwa ba cewa ‘yan jam’iyyu na daban daban sun zo kuma da Malaman Addini sun zauna gaba daya. Yawanci za ka ga ba a fiya haduwa ba a irin wannan fanni.
Amma Alhamdulillahi mutane sun yaba kuma wadansu sun ba da shawarwari nan gaba in an tashi akwai wadanda a ka manta ba a kirawo ba, ya kamata su ma a ce an kira su kamar jami’an tsaro kenan. Domin su sheda wannan bitar a ce har da su. Wasu sun yi kira cewa kamata ya yi a ce an kira shugabannin masu ruwa da tsaki, da bangaren masu zartarwa, masu gudanarwa sannan da su kansu fannin malaman. A ce an fadada an kira kowane bangare nasu don su samu halarta. Abin gaskiya ya ba da shaawa. Kuma wallahi mutane sun kira kuma abun ya samu publicity sosai ya yadu ya kai har inda ba a taba zata ba.
3. Tambaya : A takaice me kake gani za a iya cewa shine babban amfanin da wannan taro ya haifar? Musamman ganin irin muhimman mutanen da taron ya hada.
To Alhamdulillahi na yi matukar farin ciki kuma na ji dadi da a ka ce mu ne mu ka fara assasa irin wannan. Kuma ka ga muhawarar da a ka ta karawa juna sani, a ka yi ta karawa juna fahimta. Kuma an tsaftace wannan tsari kuma ‘yan siyasa da yawa abun ya burge su ya ba su sha’awa matuka. Kuma wadansu sun ce za su kwaikwaya su yi a mazabunsu da kuma wurarensu. Sun yarda cewar in a na irin wannan a na kara fahimta a na karawa juna sani a na kara fahimtar da su kansu ‘yan social media, tabbas za a samu tsafta a cikin wannan tsari.
Kuma za a daina fitintinu, kuma a daina rigingimu, a daina cin mutuncin juna. Kuma zai kara ba mu hadin kai ko a wacce jam’iyya mutum ya ke za a yi adawa mai tsafta. Adawa halal ce a siyasa ka fadi inda a kai kuskure domin a gyara. Tunda in ba adawar ba za a yi gyara ba. Kuma shugabanni ba za a yi kira a gare su, su san ma mai takala yake ciki ko kuma wanda suke mulka ya ke ciki ba. Tun da in ka kalla wurare da fadi wurare da girma ba ko ina ne hannun gwamnati zai iya kai wa ba. Amma tun da akwai wannan kafafen sada zumunci na social media shi ne za ka ga wani shugaba ya ga halin da a ke ciki. Kuma har a kai dauki a kawo gyara a wannan wuri.
Kuma ina kira ga ‘yan siyasa yan uwana da mu ci gaba da irin wannan muhawara mu ci gaba da irin wannan tarurruka domin mu kawo tsafta mu kawo gyara a cikin wannan tsari na social media. Kuma mu dinga hada zumunci tun da wani dan social media bai ma san dan uwansa dan social media ba sai an samu irin wannan tsarin za ka ga an hadu an zo an zauna an karawa juna fahimta, an karawa juna sani.
Musamman irin wadannan malamai da mu ka kira da masana a wannan fanni dan sun zo sun ba da ilimi dan wani ma ba za ka taba ganinsa ba sai a irin wannan wuri ko kuma a aji ko a makaranta ko a wani taro. Amma ka ga mun tara su sun zo sun bayar da ilimi irinsu shi Sheikh Ibrahim Khalil su yi Dr Aminu Daurawa, su Farfesa Abdallah Uba Adamu, da sauransu shugabanni masu girma da sanin yakamata.
4. Tambaya : Yaya kake kallon amfanin irin wannan hobbasa a shekaru masu zuwa? Musamman ga al’ummar mu da kuma yanayin zamantakewa, musamman a bangaren siyasarmu.
Ai ni kiran da nake yi shi ne wannan harka ta social media ita ce abinda muke tsinkaye nan gaba, (future), wato ga ta nan kamar wutar daji. Abu na faruwa yanzu za ka gani. Yanzu ma mutane sun rage kallon Talabijin. Dama can iyayenmu da kakaninmu su na sauraron radio har yanzu ba a daina yayin radio ba.
To da harkar social media da radio sun fi Talabijin don ba kowa ne za ka ga ya na da akwatin Talabijin a gidansa ba. Amma ba za ka rasa mutum ya na da ‘yar waya ba wadda yake zagayawa shafukan sada zumunta ya na shiga ya ga mai duniya take ciki.
Kuma yanzu an ci gaba, mutum daga Nijar da Chadi da Ingila da Amurka sai ka ga a na magana da shi kai tsaye ba wani shamaki, don ma ya san me gida yake ciki.
Saboda haka kira da na ke yi shi ne gaba daya sai mun hada hannu da karfi, sannan kuma wadannan gidajen Talabijin ko gidajen yada labarai su hada kai da mu domin mu ci gaba da tsaftace wannan harka ta social media.
Abu ne ba mai sauki ba, saboda kullum samun mutane a ke su na kara tsunduma a cikin wannan harkar. Musamman matasa da suke tasowa. In ba a irin wannan bita a na karawa juna sani, a na tsaftace wannan harkar, to za mu tsinci kanmu a cikin wani yanayi ko cikin wani hali da ba ma so.
Kuma shugabanni dole sai sun kara dagewa sun kara tsayawa domin a fahimtar da al’umma wannan, musamman gwamnatoci da suke mulki. Dole a wayar wa da mutane kai sannan talaka ya san ya a ke gudanar da mulkin, kuma ya samu hanyar da zai dinga kai kokensa yadda za a zo a yi gyara.