Sanatoci Nigeria Sun Dage Zamansu Bayan Rikici Kan Sauyin Kujeru A Zauren Majalisa.

Spread the love

Majalissar dattijan Nigeria, ta dage zaman ta, har zuwa ranar 7 ga watan Mayu 2024, domin samun damar sake gyara zauren majalissar.

Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa, daukar matakin ya biyo bayan dawowar majalissar daga hutu, inda ta fuskanci wasu matsaloli na rashin ingancin sautin murya a zauren majalissar.

Mataimakin shugaban majalissar Dattawan Nigeria, Sanata Barau I. Jibrin, ne ya jagoranci zaman majalissar, inda ya ce majalissar dage zaman har zuwa ranar 7 ga watan Mayu 2024, don kammala aiyukan zauren majalissar.

Tsarin wajen zama a zauren Majalisar Dattawa da aka yi a ranar Talata ya raba kan sanatoci a lokacin da suka koma zama a babban zauren majalisar bayan da aka jima ana gyara wa.

Bayan kammala aikin gyaran ne suka koma zauren da aka gyara domin gudanar da harkokinsu, bayan sun shafe kusan kwanaki 40 suna hutu.

Rikicin dai ya faro ne a lokacin da Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya fara fitar da sunayen sanatocin da suka yi bikin zagayowar ranar haihuwarsu a lokacin hutun.

Musamman Sanata Sahabi Alhaji Ya’u, ya tashi daga kujerar da aka ware masa domin ya kai korafi ga shugaban masu rinjaye, Sanata Micheal Opeyemi Bamidele, cewa bai ji daɗin kujerar da aka ba shi ba.

Lamarin da ya yi korafin ya janyo kakkausar suka daga Bamidele, lamarin da ya kai ga sanatocin biyu sun yi musayar kalamai a cikin wani yanayi mara daɗi.

Hakan dai ya koma musayar yawu, sakamakon haka ya tilastawa sanatoci yin gaggawar shiga wani zama na sirri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *