Rashin isassun jami’an tsaro ne ke haifar da karuwar hare-hare a Kaduna – Uba Sani

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce babu isassun jami’an tsaro a yankunan da ke fama da hare-hare a jihar, lamarin da ya ce shi ne babban dalilin karuwar garkuwa da mutane a yankunan.

Gwamnan ya shaida wa BBC cewa kusan daliban makarantar Kuriga da aka sace 28 ne suka kubuta daga hannaun ‘yan bindigar da suka sace su.

Tuni dai sojojin Najeriye karkashin kulawar babban hafsan sojin kasa ke ci gaba da neman sauran yaran tare da hadin gwiwar ‘yan sanda da mafarauta a dazukan Kaduna da jihohin Zamfara da Katsina masu makwabtaka.

Su ma a nasu bangaren iyayen yaran da aka sacen sun kafa kungiyoyin ‘yan sa kai tare da neman agajin gaururuwan da ke makwabtaka da Kuriga ko za su samu labarin inda ‘ya’yan nasu suke.

Matsalar Satar Mutane Ma su Yawa ta sake Kunno Kai A Nigeria

Matar Kwamishinan Yan Sandan Kano Ta Tallafawa Membobin POWA 100.

Nan gaba a yau ne ake sa ran mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar don ganawa da gwamnan, bisa umarnin shugaban kasa na kubutar da yaran.

Ana ci gaba da samun karuwar fargaba daga bangaren iyayen yara a yankin arewacin Najeriya, kan tsaron lafiyarsu a makarantun.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *