Rashin Tsaro: Hanyar Gusau zuwa Funtua ta zama tarkon mutuwa

Spread the love

Garuruwan da ke kan babbar hanyar Gusau zuwa Funtua sun nemi ƙarin ɗaukin hukumomi saboda ƙamarin hare-haren yan fashin daji da ke buɗe wa matafiya wuta suna satar fasinjoji.

A baya baya nan dai lamarin tare hanyar da kai hare-hare ba ji ba gani kan motoci a babbar hanyar wadda ke haɗa jihohin ƙuryar arewa maso yamma da sauran sassan Najeriya ya ƙara ta’azzara, duk da ɗumbin shingayen binciken jami’an tsaro.

Rahotanni sun ce ko a ranar Lahadin da ta wuce ƴan bindigar sun kai mummunan hari inda suka harbi kwamandan rundunar ƴan sa-kai na Askarawan Zamfara wanda a halin yanzu yake jinya a asibiti.

Haka kuma, wata sanarwa daga gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa a makon jiya ma ƴan bingidar sun yi wa wasu jami’an rundunar Askarawan kwanton ɓauna a yankin Tsafe, inda suka kashe tara a cikinsu.

Mazauna yankin dai sun ce duk da yawan shingen bincike na jami’an tsaro, amma kusan kullum sai yan bindiga sun kai hari tare da sace mutane, lamarin da ya haifar da fargaba, kamar yadda wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC.

”Muna yawan samun hare-haren ƴan bindiga a kan wannan hanyar, inda a wasu ranakun ma sukan kai hari fiye da ɗaya, wannan ta sanya mu cikin wani irin halin na matuƙar fargaba, domin hanyar ta koma yanzu kusan duk wanda zai bi ta sai dai ya yi shahada don yana iya haɗuwa da waɗannan mutanen ya kuma rasa rayuwarsa”. in ji shi

Mazaunin ya ƙara da cewa ƴan bindigar sukan tare hanyar ne su fara harbin kan mai uwa da wabi daga bisani kuma su sace na sacewa su shige cikin daji.

Wannan matsala da ta addabi wannan hanyar ta shafi yankuna da al’ummomi da dama saboda hanya ce da mutanen jihohin Zamfara da Kebbi da Sokoto da Katsina da wasu yankunan Jamhurriyar Nijar ke amfani da ita wajen gudanar da kasuwanci da sauran harkokin yau da kullum.

Hukumomin Najeriya dai sun sha iƙirarin cewa suna ɗaukar matakai domin magance wannan matsalar duk da yake ana ganin har yanzu lamarin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

A wata hira da ya yi da BBC, Gwamna Dauda Lawal Dare na Zamfara ya tabbatar da harin da aka kai kan rundunar askarawan inda ya ce gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a yaƙin da take yi da ƴan fashin dajin.

”Wannan abin da ya faru ba zai tsorata mu ba, kuma ba zai sa mu daina abin da muke yi na tabbatar da cewa an samun zaman lafiya a jihar Zamfara ba.” in ji shi

Gwamnan ya ƙara da cewa a ko da yaushe yana tattaunawa da shugabannin tsaro don ganin yadda za a bullo da sabbin hanyoyin daƙile ƙaruwar hare-haren ƴan fashin daji musamman a hanyar Gusau zuwa Funtua.

Ya bukaci a cire batun siyasa a yaƙin da ake yi da lamarin rashin tsaro inda ya bayar da tabbacin cewa ƙofarsa a buɗe take domin karɓar shawarwari da gudunmawa kan yadda za a shawo kan matsalar.

”Ba na sanya siyasa a cikin batun yaƙi da rashin tsaro.

Zan yi baƙin ciki a ce na rasa wani ɗan Zamfara. Babu batun siyasa a ciki, duk wani wanda yake da wata rawar gani da zai taka ta kawo sauƙin wannan matsala, ni a shirye nake in saurare shi,” gwamnan ya ce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *