Kungiyar likitocin Najeriya NMA ta umurci likitocin da ke asibitin yara na Hasiya Bayero da ke Kano da su dakatar da ayyukan da suke yi saboda fargabar fuskantar hare-hare da rashin tsaro.
Sakataren kungiyar NMA reshen Kano, Dr. Abdulrahman Aliyu ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ƙungiyar ta yi ƙarin bayani kan wani mummunan lamari da ya faru a ranar 27 ga watan Mayu, inda wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai wa wasu likitoci mata biyu hari tare da yi musu barazana da bindiga.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wasu mutane ɗauke da makamai sun kai wa likitocin da suke gudanar da ayyukansu hari inda suka kutsa cikin ofishinsu da karfi tare cin zarafinsu da yi musu barazana, sannan kuma suka nuna musu bindiga.”
Aliyu ya ƙara da cewa, an shafe kusan sa’a guda ana rikicin ba tare da samun wani taimako daga jami’an asibitin ko hukumomin waje ba.
Ya kuma yi karin haske kan wani lamari da ya faru a baya a farkon wannan shekarar, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jami’in kiwon lafiya da ke bakin aiki a sashen masu haihuwa na Asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano.
Irin wadannan al’amura sun yi tasiri matuka wajen sanya tsoro da zaman ɗar-ɗar a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya a jihar, in ji Aliyu.
BBC HAUSA
- Gwamnan Kano ya gana da Nuhu Ribadu
- Ba Zan iya kamanta yadda naji lokacin da Gwamna yabani shugabancin KSSMB :Dr. Kabir Zakirai