Rashin Wutar Lantarki Barazana Ce Ga Tsaron Nigeria – Alh. Halifa Bala Rabi’u

Spread the love

Tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta Janye Tallafin wutar lantarki kuma daga baya ta sanar da Shirin ta na kara kudin wutar , al’ummar Nigeria suka shiga halin dimuwa saboda zaman wutar a sahun abubuwan da dan Nigeria ke mora a halin yanzu.

To sai dai wasu masana na kallon lamarin inganta wutar a matsayin wani abu dake cike da shakku saboda yadda Gwamnati ta bayyana wasu abubuwa da ta ce idan tayi wutar zata wadata , sai gashi tsawon lokaci shiru kakeji.

Da yake tattaunawa da Jaridar Idongari.ng a Safiyar Talata 14 ga watan Mayun 2024, Shugaban Kamfanin *Halba Plastic and Recycling* Company dake unguwar Dakata a Jihar Kano, Alh. Halifa Bala Rabi’u ya bayyana irin Damuwar da suka shiga sakamakon Rashin wadatuwar wutar a Jihar Kano.

” Gaskiya bamu ji dadi ba da karin farashin wutar lantarki da gwamnati tayi, saboda ko me kake sarrafawa babu yadda za’ai ka karawa Customer dinka kusan ninkin uku akan abinda aka kara maka, saboda wanda yake biyan Miliyan 2 a wata ya koma yana biyan Miliyan 6 da doriya, gaskiya hakan ba abu bane me kyau;”.

” Gaskiya yanzu mutane da dama ba zasu iya biyan wannan kudi ba saidai kawai su rufe kamfanonin su don wasu ma sun fara, kuma gwamnati kullum tana Magana zata samarwa matasa aiki za’ai abubuwa da yawa amma kuma bata yi kananan masana’antu sun samar da guraben aikin kuma azo musu da wani tsari s firgita su , gaskiya inaga hakan babu Adalci , mu bamuce gwamnati kada tayi kari ba saboda ita ma kudi take kashewa amma fa a duba aga me Za’ayi akai”.

Jaridar Idon gari ta Ruwaito Alhaji Halifa Bala Rabi’u na cewa, akwai babban hadari ga al’umma dama gwamnati idan kamfanoni irin nasu dake da matasa fiye da dubu daya suka Dena aiki sakamakon Rashin wadatuwar lantarkin.

” Nidai shawara ta gwamnati shine azo a zauna a duba abinda ya kamata, don idan wadannan matasa suka rasa aiki kuma Ba’a tanadar musu wani abu ba to ba shakka ita ma gwamnati tana cikin barazanar tsaro, saboda zasuje su sanarwar kansu wani aikin , kuma aikin da zasu samu ba lalle bane me kyau ne”.

Idan za’a iya tunawa ko a ranar Litinin 13 ga watan Mayun 2024, sai da wasu mambobin kungiyar kwadago ta kasa suka rufe Hanyar shiga ofishin hukumar samar da wutar lantarki ta kasa dake Abuja domin nuna rashin gamsuwar su da yadda kullum lamarin wutar ke kara tabarbarewa a Nigeria.

IDONGARI.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *