Real Madrid ta ci gaba da zama a saman teburin La liga bayan da ta doke Osasuna da ci 4-2 a wasan mako na 29.
Real ta fara cin kwallo ne ta hannun ɗan wasanta na gaba Vincius Junior a minti na 4 da fara wasa.
Sai dai ba a jima ba Osasuna ta farke ta hannun Budimir a minti na 7.
Madrid da ta kai ziyara gidan Osasuna ta ci kwallo ta biyu a raga ta wajen ɗan wasanta na baya Dani Carvajal, inda wasan ya koma 2-1.
Bayan dawowa hutun rabi lokaci, Brahim Diaz ya ci wa Real kwallo ta uku a minti na 61.
Jim kaɗan kuma Vinicius Jr ya ci kwallonsa ta biyu ta huɗu kuma wanda Madrid ta ci Osasuna.
Real ta ci gaba da zama a kan teburin La liga da tazarar maki 10 tsakaninta da Girona da ke matsayi na biyu da maki 62, kafin wasanta da Getafe.
An kashe sojojin Najeriya 15 a Delta