Rikicin Soyayya: Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi Da Cakawa Saurayi Wuka A wajen Budurwa

Spread the love

Kano

Rundunar Yan Sandan jahar Kano ta kama wani matashi , Ibrahim sabo Kurna, da ake Zargi da cakawa wani Wuka a sassan jikinsa lokacin da yake zance da budurwarsa a Unguwar Bachirawa dake jahar.

Lamarin ya Faru ne a ranar Asabar din da ta gabata da misalin karfe 8:30PM na dare.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa , sun samu korafi ne Daga wajen Yayan Saurayin da aka Jiwa raunukan, da cewar Wani Mai suna Ibrahim Sabo mazaunin unguwar Kurna, ya caccakawa Kaninsa Sulaiman Muhammed, Wuka a sassa jikinsa da suka hada da, Kansa, Hannun Hagu da kuma kafarsa.

Bayan Samun korafin ne Rundunar Yan Sandan ta Kai matashin asibitin Shehu Waziri Gidado, Inda aka duba lafiyarsa.

SP Abdullahi Kiyawa, yanzu haka sun cafke Wanda Ake Zargin , kuma an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba, kawo yanzu na cewa shi ma Wanda Ake Zargin Saurayin budurwar ne .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *