Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama matasa masu tarin yawa, a unguwar sheka, sakamakon ricikin fadan daba da ya kaure a tsakanin su.
Kakakin Rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ricikin ya barke ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu Sheka Babban Layi, da ake zargi da laifin fashi da kuma laifukan daba a unguwar Sheka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin yana cikin gungun matasan da ake kira da Yan shida wadanda suka addabi Sheka da fashi da kuma fadan Daba.
Al’ummar unguwar ne suka kama shi sannan suka karya kafarsa daya tare da yiwa dayar raga-raga lamarin ya da kai ga ya rasa ransa kamar yadda kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano ya sanar.
Rundunar ta kara da cewa abokan marigayin ne suka fito daukar fansar , Inda fadan Daba ya rincabe har aka kama mutane ma su yawa.
Wakilin mu da ya ziyarci unguwar ya bayyana mana cewar al’amura sun lafa sakamakon baza jami’an tsaro da aka Yi a yankin don tabbatar da zaman lafiya.