Rikicin siyasar jihar Rivers ya ɗauki wani sabon salo a ranar Lahadin ƙarshen makon nan tun bayan da gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 23 da aka zaɓa ranar Asabar, abin da kuma ya janyo ƴan jam’iyyar PDP ɓangaren Nyeson Wike da na APC suka garzaya kotu suna ƙalubalantar zaɓen.
Jam’iyyar APP dai ita ce ta lashe kujeru 22 daga cikin ƙananan hukumomin jihar guda 23.
Tun bayan da uwar jam’iyyar PDP ta miƙa wa Nyesom Wike ragamar jagorancin jam’iyyar PDP a jihar Rivers ne dai wasu daga cikin ƴan jam’iyyar PDP, ciki har da waɗanda gwamna Fubara ya naɗa shugabannin riƙon ƙwarya a ƙananan hukumomin jihar bayan wa’adin mutanen Wike ya ƙare suka koma jam’iyyar APP.
Komawarsu APP ke da wuya suka samu tikitin takarar shugabancin ƙananan hukumomi a zaɓen da aka yi ranar Asabar.
Hakan ya sa ake tunanin wataƙila gwamna Fubara ne ya tura su can, kasancewar PDP ba a hannunsa take ba.
Masu lura da al’amuran siyasa sun ce gwamna Siminilayi Fubara ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin a ranar Lahadi domin tsoron ka da a samu wani hukunci daga wata kotu da zai hana rantsarwar.
Atiku da gwamnoni sun taya Fubara murna
Wasu jiga-jigan mam’iyyar PDP ta taya gwamna Fubara murnar lashe zaɓen ƙananan hukumin na ranar Asabar, duk da cewa jam’iyyar PDP a jihar ba ta shiga zaɓen ba.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya taya gwamnan murna inda ya ce nasarar da Fubara ya samu na nuni da irin yadda al’ummar jihar Rivers suka gaji da siyasar zalunci da siyasar ubangida a jihar.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Atiku Abubakar wanda Wike ya yi takara da shi a zaɓen cikin gida na neman takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ce yanzu jihar Rivers za ta ɗauki saiti wajen gudanar da mulkin dimokraɗiyya ba tare da shisshiga.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda kuma shi ne shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP ya kasance a wurin rantsa da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin.
Mai laya kiyayi mai zamani
Dakta Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami’ar Abuja ya kwatanta abin da ya faru a jihar ta River a ƙarshen mako da ‘mai laya kiyayi mai zamani’.
“Abin da wannan ke nuna shi ne tagomashi da karsashin Wike na dakushewa a jihar bisa la’akari da yadda gwamnan ya aika mutanensa sabuwar jam’iyyar amma kuma cikin lokaci ƙankani sai ga shi jam’iyyar ta yi nasara.”
Dakta Kari ya ƙara da cewa “kusan duk wani mai faɗa a ji a jihar yana tare da Fubara. Sannan kuma ka dubi yadda jama’a suka fito sosai domin kaɗa ƙuri’a. Duk waɗannan alamu ne da ke nuna yadda Fubara yake ta ƙara samun karɓuwa.
Kai hatta Atiku Abubakar ya aike da saƙon murna. Haka ma wasu gwamnoni misali gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya je rantsuwar shugabannin. Sannan alamu na nuna tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a kaikaice yana tare da Fubara.” In ji Dakta Abubakar Kari.
Rundunar ƴan sandar jihar Rivers ta janye jami’anta daga dukkan sakatariyar ƙananan hukumomi 23 da ke jihar, hakan na zuwa ne bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomin tare da rantsar da wadanda suka yi nasara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar ƴansandar, Grace Iringe-Koko , ta fitar da safiyar yau Litinin ta tabbatar da hakan.
Ta ce kwamishinan ƴansanda na jihar ya bayar da umarnin ne ƙarƙashin umarnin Sifeto Janar, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci a janye jami’an da ke samar da tsaro a dukkan hedikwatar ƙananan hukumomin jihar nan take.
Jami’an ƴansanda dai sun ƙarɓe iko da hedikwatar ƙananan hukumomi a watan Yuni sakamakon rashin fahimta da ta shiga tsakanin Kantomomi masu goyon bayan gwamnan jihar mai ci Siminalayi Fubara da kuma tsoffin shugabannin ƙananan hukumomin na gwamnatin da ta gabata da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.