Rt Hon. Kabiru Rurum Da Sanata Kawu Sumaila Sun Kai Ziyara Rano Don Jajantawa Kan Abunda Ya Faru .

Spread the love

 

A wannan rana ta Asabar Maigirma Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum da Dist Sen Abdurrahman Kawu Sumaila sun ziyarci Karamar hukumar Rano don jajantawa game da lamarin daya faru kwanakin baya na rikici daya yi sanadiyar rasuwar yaro guda da Kuma DPO yankin.

Yayin ziyarar, RT Hon Kabiru Alhassan Rurum da Sanata Kawu Sumaila sun xiyarci ofishin ‘yan sandan dan ganin barnar da akai sannan sun ziyarci Ofishin shiyya na ‘yansanda dake ranon dan ganawa da (Zonal Commander).

Tawagar ta Kuma ziyarci Maimartaba Sarkin Rano Alh Isah Ummaru dan jajanta masa sannan sun ziyarci iyayen yaron daya rasa ransa.

Dist Sen Abdurrahman Kawu Sumaila da RT Hon Kabiru Alhassan Rurum sun yi Alkawarin gyara wuraren da suka lalace a Ofishin ‘yan sanda na Rano sannan Sunyi Alkawarin cigaba da samarda ababen more rayuwa da kayan aiki ga Jami’an tsaro na yankin..

Sun Kuma bukaci a samar da kyakykyawar alaka tsakanin Al’ummar garin da Jami’an tsaro tare da kira ga iyayen yara su rinka jan kunnen ‘ya’yansu kaucewa daukar doka a hannu..

Tawagar ta RT Hon Kabiru Alhassan Rurum na tare da wasu cikin ‘yan Majalisar Wakilai ta kasa da tsoffin ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano da shugabannin Jam’iyyar APC na kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure..

*Fatihu Yusuf Bichi*
*SSA Media & Publicity*
*June 21st, 2025.*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *