Rufe iyakar Nijar yana cutar da tattalin arziƙin Najeriya — Sanata Aliero

Spread the love

Ɗan majalisar dattawa da ke wakiltar tsakiyar jihar Kebbi, Sanata Adamu Aliero, ya bayyana cewa ci gaba da rufe iyakar Jamhuriyar Nijar yana cutar da tattalin arzikin jihohin Najeriya da ke mawakbtaka da ƙasar.

Aliero ya faɗi haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Arise, inda ya ce rufe iyakar Nijar bisa umarnin da ƙungiyar Ecowas ta bayar a matsayin abin da bai dace ba da kuma ya kamata a sake dubawa.

Ya ce ƴan majalisa daga jihohin da abin ya shafa da ke arewacin ƙasar sun zauna sun tattauna kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta buɗe iyakar da gaggawa domin ci gaba da harkokin kasuwanci.

“Mutanen mu da ke zaune cikin al’ummomi da ke makwabtaka da iyakar Nijar su ne waɗanda ke ɗanɗana kuɗarsu.

“Idan ka je kan iyakar a yau, za ka ga ɗimbin motocin dakon kaya da ke dawowa tare da kayayyaki daga ƙasashe daban-daban na tsaye a kan iyaka sun ƙasa wucewa saboda takunkumin Ecowas,” in ji ɗan majalisar.

Ya ce an take yarjejeniyar da aka cimma da Nijar kan yashe madatsar ruwan da ke samar da wutar lantarki lokacin da gwamnati ta yanke shawarar katse hanyoyin samar da wutar lantarki ga Nijar ɗin.

Sanata Aliero ya ce yawancin ƙasashe ba su saka wa Nijar takunkumi ba kamar yadda Ecowas ta yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *