Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama riƙaƙƙun ‘yanbindiga a jihar Taraba

Spread the love

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama wasu ƙasurguman ‘yanbindiga biyu a jihar Taraba da ke tsakiyar ƙasar tare da ƙwace babura daga hannunsu.

Wata sanarwa da mataimakin kakakin runudunar, Kanal Oni Olubodunde, ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ne suka yi nasarar kama mutanen da ba ta bayyana sunansu ba a ranar Alhamis.

“Samamen da dakaru suka kai bayan tattara bayanan sirri a ƙauyen Geshi na ƙaramar hukumar Donga a jihar Taraba ya yi sanadiyyar ƙwato babur biyu da ‘yanta’addan ke amfani da su,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa an samu bayanan sirrin ne bayan wasu mahara sun kai hari, inda dakaru suka ɗunguma zuwa Geshi kuma suka fara musayar wuta da su “abin da ya sa suka tsere zuwa cikin daji”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *