Rundunar sojin Najeriya ta kammala bincike kan harin Tudun Biri

Spread the love

Rundunar Sojan Najeriya ta ce nan da karshen wannan watan za a samu sakamakon binciken aka yi kan harin maras matuki da sojojin kasar suka kai kan kauyen Tudunbiri da ke jihar Kaduna.

Akalla mutane 85 suka rasa rayukansu a cikin hare-hare biyu da jirgin mallaKin Rundunar sojan kasa ta kasar ya kai kan taron masu maulidi a watan Disamban da ya wuce, Lamarin da ya jawo Karaye-kirayen a yi bincike akai.

A cewar Babban Hafsan tsaron kasar Janar Chris Musa an kawo karshen binciken in ban da dan abin da ba a rasa ba kuma shirye suke su fitar da sakamakonsa nan da karshen wannan watan na Febrairu.

‘‘Dama akwai abubuwan da ake buƙata; sunayen waɗanda suka mutu, abin da ya samu wanda ya ji ciwo, shi ne muke ƙoƙarin samu amma ba mu iya samun duka ba saboda wasu an riga an binne su. Ba abin da kuma za mu je mu tono bane don ba mu son dawo da abin da ya riga ya wuce. To amma report a shirye yake, in Allah ya so kafin ƙarshen wata za a fitarwa mutane su san abin da ya faru.’’

Ya dai jaddada cewa rundunar sojin Najeriya ba zata gaji ba wajen gudanar da aikin ta na kare jama’a da kuma kawar da ɓata-gari. Sannan ya maimaita matsayar sa tun farko, cewa abin da ya faru a Tudun Biri kuskure ne aka samu.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama dai na gaba wajen kiran da a binciki wannan lamarin domin gano wadanda ke da hannu a ciki da yadda aka yi ya faru domin yi wa wadanda lamari ya sha adalci da hukunta masu hannu a lamarin da kuma kare faruwar hakan a gaba.

Kan haka ne na nemi jin ta bakin Isa Sanusi, daraktar kungiyar Anmesty International kan cimma wannan gabar da aka yi.

‘‘Za mu jira mu ga abin da sakamakon binciken ya ce da kuma abin da aka gano. Muna da tarihi na cewa jami’an tsaro idan wasu daga cikin su suka yi laifi sai su canza masu wajen aiki ko su ɗauke su zuwa wata jiha. Muna fatan wannan bincike na gaskiya ne, kuma muna fatan Allah ya sa ya kai ga hukunta duk wanda ke da hannu a cikin abin da ya faru a Tudun Biri.’’

Gamayyar hukumomin tsaro a Kano sun tattauna da shugabancin jam’iyun siyasa gabanin zaben cike gibi da za a sake yi a Kunchi/Tsanyawa.

Isa Sanusi ya ce duk wani bincike na gaskiya to kamata ya yi, ya zamo ya bayyana gaskiya, sannan kuma ya kamata binciken ya yi hukunci, wato ya gano masu laifin ya kuma hukunta shi, sannan kuma ya zamo ya ɗauki matakin kada a ƙara maimaita abin da aka yi a baya.

A daren ranar Lahadi ta uku ga watan Disamban bara ne dai wani jirgi mara matuki mallakar sojojin Najeriya ya kai hari bisa kuskure har sau biyu kan dandazo mutane da ke hallatar taron Maulidi a kauyen na Tudun Biri da ke jihar Kaduna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100 da kuma raunata wasu masu dimbin yawa.

Kuma kimanin makonni biyu bayan faruwar lamarin hedikwatar tsaron kasar ta sanar da kafa wasu kwamitoci biyu domin bincikar baya ga wanda gwamnan jihar Kaduna ya bayar da umarnin a yi jin kadan bayan afkuwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *