Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya buƙaci sojojin Najeriya su fatattaki Lakurawa daga jihohin Sokoto da Kebbi da ke arewacin ƙasar.
Wata sanarwa ta ce babban hafsan ya bayyana haka ne a cikin saƙon da ya aike wa runduna ta musamman da ya tura domin aikin fatattakar Lakurawa mai suna “Chase Lakuwaras Out”.
Da yake jawabi a madadin babban hafsan, babban kwamandan runduna ta 8 ta sojin ƙasa na Najeriya, Birgediya Janar Oluyinka Soyele, ya buƙaci sojojin su tabbatar sun kawo ƙarshen ƴan ƙungiyar.
Sai dai ya buƙaci sojojin su kiyaye rayuka da dukiyar al’umma na waɗanda babu ruwansu.
A cewarsa: “An zaɓi sojojin ne sannan aka horar da su, don haka ƴan Najeriya suna fata za su fatattaki Lakurawan nan baki ɗaya,” kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya nuna.
Mr Soyele ya ce tun kafin aika sojojin na musamman, dakarun rundunar sun kutsa dazukan Sokoto da Kebbi, inda suka gwabza da ƴanbindigar, inda suka ƙwato bindigu da alburusai da dama.