Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin ɗaukar fansar kisan dakarunta shida

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin ɗaukan fansa kan kisan da aka yi wa sojojinta shida bayan yi masu kwanton ɓauna yayin da suka je jihar Neja domin aikin kwantar da tarzoma.

Sojojin sun je aiki ne ƙauyen Karaga a yankin Shiroro ranar Juma’a inda wasu da rundunar ta kira ƴan ta’adda suka kai masu hari.

Wata sanarwa daga rundunar sojin ta ce an kashe da dama cikin maharan sannan kuma ana neman wasu a cikinsu.

Rundunar ta yi alƙawarin ɗaukar fansa kan kisan sojojin.

Sojojin da aka kashe sun haɗa da manyan jami’an soji biyu da wasu sojoji huɗu, a cewar rundunar.

Sojoji biyu sun ji rauni a harin.

Rundunar ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani jami’in soji.

Babu ƙarin bayani game da waɗanda suke da hannu a harin amma ana zargin ƴan bindiga da hannu a kai wa jami’an tsaro hare-hare a baya-bayan nan.

Harin ya zo ne yayin da Najeriya ke karɓar baƙuncin taron yaƙi da ta’addanci a Abuja, babban birnin ƙasar.

Harin kwanton ɓaunan ya so ƴan makonni bayan kisan sojoji 16 a lokacin da suke wanzar da aikin zaman lafiya a tsakanin wasu al’umomi da ba sa ga maciji da juna a jihar Delta.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da suka shafi yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke kai hare-hare a sassan ƙasar sai dai hukumomi sun sha bayyana irin ƙoƙarin da suke na magance ƙalubalen da tsaron ƙasar ke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *