Rundunar Sojin Saman Nigeria Za Ta Yi Bincike Kan Zarginsu Da Kashe Fararen Hula A Zamfara

Spread the love

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan wasu rahotannin da suka ce an kashe fararen hula a yayin wani harin da aka kai a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar a karshen makon da ya gabata.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin darektan sashen hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ta ce an kai harin ne kan wasu ƴan bindiga a yankin Tungar Kara da ke ƙaramar hukumar Zurmi a jihar ta Zamfara inda aka yi nasarar kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, duk da ya ke harin ya yi nasarar tarwatsa wani sansanin ƴanbindiga da suka addabi yankin, rundunar ta nuna matuƙar damuwa kan rahotannin rashin rayukan fararen hula da aka samu inda ta ƙara da cewa tana kan gudanar da bincike kuma za a sanar da sakamakon hakan da zaran ya kammala.

Ta kuma bayar da tabbacin cewa zata ci gaba da ɗaukar matakai da za su tabbatar da cewa an kiyaye rayukan fararen hula a yayin da ta ke ƙokarin tabbatar da ingantaccen tsaro a sassan ƙasar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai mazauna yankin na Tungar Kara suka ce aƙalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon harin sojoin, ciki ma har da ƴan sintirin da ke ƙoƙarin yaƙar ƴanbindigan.

A cikin watan Disamba aƙalla mutane 10 ne suka mutu a lokacin da wani jirgin yaƙin soji ya kai hari bisa kuskure kan wasu fararen hula a jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *