Rundunar Sojojin Nigeria Ta Samar Da Nambar Kira Ga Jama’a Don Yaƙar Yan Bindiga.

Spread the love

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samar da hanyar sadarwa tsakaninta da jama’a domin yaƙar ƴanbindiga musamman a jihohin Zamfara da Kebbi.

Wata sanarwa da rundunar sojin da ke yaƙi da masu fashin daji da satar mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya ta fitar, ta ce ta samar da wani layin wayar tarho da jama’a za su rika kira kyauta, ba tare da an caje su kuɗin kira ba, domin a rika sanar da jami’anta bayanan da ke buƙatar kulawar gaggawa.

Ta ce wannan yana daga cikin ƙarin matakan da rundunar ke bi wajen ganin an shawo kan matsalar hare-haren ƴanbindiga da suka addabi yankin.

Kamar yadda matsalar hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar jama’a a A Rundunar Operation Hadarin Daji da ke gudanar da ayyukan samar da tsaro a yankin, ta ce wannan wata sabuwar dabara ce da za ta kara taimakawa ta fuskar sadarwa tsakanin rundunar da jama’ar garuruwan da ke fama da wannan jidali.

“An kaddamar da wani sabon layin wayar tarho mai lamba 080-000-2020-2 domin jama’a su riƙa kiran jami’an tsaron su isar da sakon gagawa da ƙorafia da kuma neman taimkon gaggawa,” in ji sanarwar.

Rundunar sintirin ta Operation Hadarin Dajin ta yi kira ga jama’a da su yi kyakkyawan amfani da wannan damar da ta dace, wajen samar da bayanai a kan kari, kuma sahihai, waɗanda za su taka muhimmiyar rawa a fafutukar yaƙin da take yi da ƴanbindiga.

ƴanbindigar sun kwashe shekaru suna kashewa da satar mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Ko a makon nan sun kashe Sarkin Gobir na Gatawa bayan sun yi garkuwa da shi – kisan da ya tayar da hankalin Najeriya musamman bidiyonsa da aka gani ana gana masa azaba kafin samun labarin kashe shi.

Gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaro sun daɗe suna ikirarin cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan matsalar ɓarayin dajin amma kuma matsalar sai ƙara ƙamari take yi a sassan jihohin arewacin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *