Rundunar Tsaron Najeriya ta ce jami’anta sun kashe ƴan bindiga fiye da 180 tare da kama wasu fiye da 300 cikin makon da ya gabata.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran rundunar, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ce a samame daban-daban da suka kai sansanonin ‘yan bindigar a sassan ƙasar daban-daban.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun kuma ƙwato makamai masu yawa da kuɗaɗe daga hannun ‘yan bindigar.
”Haka kuma jami’an namu sun kama ɓarayin man tare da man da aka ƙiyasta cewa kuɗinsa ya kai naira miliyan N846,480,800.000”, in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa tsakanin 14 da 20 zuwa 24 ga watan Agustan, ƴan ta’adda 503 ne suka miƙa wuya, ciki har da maza 72, mata 148, da kuma ƙananan yara 283 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Janar Buba ya kuma ce dakarunsu sun kuɓutar da mutum 134 daga hannun masu garkuwa da mutane a cikin mako guda.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun ƙwato manyan makamai aƙalla 84, da alburasai guda 1,499.