Rundunar Vigilanti ta Ƙwato Shanun Sata Guda 60 da cafke masu yin sojan Gona a Jihar Kano

Spread the love

 

Yayin wasu mabanbantan samame da Jami’an Rundunar Vigilantin Jihar Kano suka gudanar, sunyi Nasarar ƙwato wasu shanu da aka sace kimanin 60.

Kakakin Rundunar Kamalu Jibril Adam Sudawa ne, ya shaida hakan ga idongari.ng  a ranar Talata a birnin Kano.

Kamalu ya ce Jami’an Rundunar tasu sunyi Nasarar ƙwato Shanun ne a Ƙananan Hukumomin Rogo da Rimin gado yayin da aka kuma kama waɗanda ake zargin.

” Munyi Nasarar kama shanu guda 60 , guda 18 daga ƙaramar hukumar Rogo kuma muka kama Ɓarayi mutum biyu daga cikin su”.

” Mun ƙwato wasu shanun guda 42 kuma daga ƙaramar hukumar Rimin gado wanda nan kuma Ɓarayi suka gudu”.

Kazalika kakakin ya kara da cewa Rundunar tayi Nasarar kama wasu Ɓata Gari a ƙwaryar birni wanda suke aikata laifuka.

Munyi Nasarar kama wasu matasa guda biyu a ƙaramar hukumar Nasarawa wanda suka ƙware wajen sayar da kayan maye da kuma yiwa Mutane ta’addanci gami da yin Sojan Gona da kayan Jami’an Vigilanti don bawa Masu laifi mafaka”.

“Munyi Nasarar Gano waɗannan matasa ne ta hanyar bibiyar Lambar Jami’an mu wadda ake kira G.I.S ta hakan ne muka gano cewa ba jami’an mu bane”.

” Bayan kammala bincike da muka gudanar mun miƙa su hannun Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano domin girbe abinda suka shuka “.

Kwamandan Rundunar Vigilantin Alhaji Shehu Muhammad Rabi’u yayi kira da Al’umma su cigaba da bawa rundunar haɗin kai don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *