Rundunar Yan Sanda Kano Ta Kai Sumame Tare Da Kama Miyagun Kwayoyi, Makamai.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan Jahar Kano, ta samu nasarar Kai sumame a yankin Hadejia road, tare da gano wasu muggan kayan maye a daddaure a Ledoji sai kuma Takobi da Adduna.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a rubutu da wallafa a shafin na Facebook a Ranar Laraba.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce wadanda ake zargi da mallakar kayan, zakara ya ba su sa’a sun cika wandunansu da iska , amma suna ci gaba sa farautarsu.

Sai dai ya shawarci ma su kayan da su Kai Kansu Helkwatar Rundunar Yan Sandan dake Unguwar Bompai Kano, ko kuma duk Wanda ya San inda suke ya taimaka wa Rundunar Wajen bata Bayan sirri domin Kamo su, ko a Kira wannan nambar 08036379054, don sanar da ita.

Idan ba a manta ba jaridar idongari.ng, ta ruwaito mu Ku , yadda Rundunar Yan Sandan Jahar Kano, ta cafke wani dilalin miyagun kwayoyi da yan tawagarsa su 8, da ake zargi da yin sarafar tabar Wiwi daga kudancin Nigeria, zuwa Jahar Kano.

Haka zalika an cafke wani magidanci da ya yi yunkurin shiga da tabar Wiwi gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya na Kurmawa Kano, don kaiwa Daurarru.

Rundunar Yan Sandan karkashin jagorancin Kwamishinan ta CP Muhammed Usaini Gumel, kwalliya ta biyan kudin Sabulu, Wajen dakile yunkurin aikata laifuka , tare da Kama wadanda ake zargin kuma an gurfanar da su a gaban kotu na daban-daban a sassan Jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *